ABNA24 : A yayin da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben kasar ta Ivory Coast, Kuibiert-Coulibaly Ibrahime ya ce shugaba Alassane Ouattara ne ya sake lashe zaben bayan ya samun kusan kashi 94.27% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Har ila yau shugaban hukumar zaben ya ce kashi 53.90 cikin dari ne na masu wadanda suka cancanci kada kuri'ar ne suka fito da kuma kada kuri’arsu.
A halin yanzu dai wajibi ne Majalisar Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da sakamakon zaɓen bayan ta saurari korafe da ake da su.
Kafin zaben dai manyan ‘yan adawa Pascal Affi N'Guessan da kuma Henri Konan Bédié sun bukaci magoya bayansu da su ƙauracewa zaben, wanda suka ce sake tsayawar shugaba Ouattara a zaben a karo na uku karen tsaye ne ga tsarin demokradiyya.
‘Yan adawan dai sun bayyana cewar sake tsayawa takara ta uku da shugaban yayi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, sai dai shi kuma shugaban ya ce yana da damar yin hakan bayan kwaskwarimar da aka yi da kundin tsarin mulkin kasar.
342/